Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.
January 09, 2023Bitar tarihin da Pele ya bari a duniyaShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh, ya tattauna da masana akan rayuwa da kuma irin gudunmawar da gwarzon dan kwallon kafa a duniya wato Pele ya bayar, tun daga zamanin da ya fara kwallon kafa zuwa lokacin da girma ya zo masa....more10minPlay
December 12, 2022Qatar 2022: An shiga mako na karshe a gasar Kofin DuniyaHar yanzu shirin 'Duniyar Wasannin' na kasar Qatar, inda ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya. Gasar taa bada mamaki ainun, duba da yadda akasarin kasashen da ake ganin za su kai baanteensu a gasar suka gaza taka rawar gaban hantsi. Yanzu haka gasar ta shiga mako na karshe, bayan da aka samu kasashen da za su fafata a matakin kusa da karshe. A ranar Lahadi ce za a buga wasan karshe na wannan gasa a tsakanin wadanda suka yi nasara a matakin kusa da karshe....more10minPlay
December 05, 2022Qatar 2022: Yadda aka karkare matakin rukuni na gasarShirin 'Duniya Wasanni' na wannan makon ya duba yadda aka fafata a wasannin karshe na matakin rukuni a gasar kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Qatar. A nahiyar Afrika, kasashe kamar su Kamaru, Ghana, Senegal da Tunisia sun fice daga gasar a matakin rukuni. A nahiyar Turai, manyan kasashe kamar Jamus da Belgium sun yi waje....more10minPlay
November 28, 2022Yadda gasar kofin duniya ta 2022 ke gudana a QatarKamar yadda aka sani, an fara gasar kofin duniya ta 2022 lami lafiya, sai dai al'ummar yankin nahiyar Afrika na kokawa kan yadda wasan ke tafiya, musamman yadda kasashen da ke wakiltar nahiyar suka gaza yin katabus a wasannin farko da suka buga. Sun koka da irin alkalancin wasa musamman a karawar Portugal da Ghana, da kuma yadda masu horarwa suka yi taa kurakurai....more10minPlay
November 21, 2022Yadda aka kaddamar da gasar cin kofin kwallon kafar duniya a Qatar 2022Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya maida hankali da wasannin gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka soma ranar Lahadi 20 ga watan Nuwambar 2022 a kasar Qatar....more11minPlay
November 14, 2022Rawar da kasashen Afirka za su taka a QatarShirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi nazari ne game da irin rawar da ake sa ran kasashen Afrika za su taka a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Qatar....more10minPlay
November 07, 2022Yadda manyan kungiyoyi suka gaza taɓuka abin kirki a gasar zakarun Turai ta 2022Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida da hankali kan yadda manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai a bana suka gaza tabuka abin kirki a gasar zakarun Turai. A ranar Larabar da ta gabata ne aka kammala wasannin rukuni na gasar zakarun nahiyar Turai, inda aka samu kungiyoyi 16 da suka kai matakin zakaye na biyu a gasar....more10minPlay
October 31, 2022Gasar motsa jiki na dakarun kare gandunn daji a YankariShirin Duniyar Wasanni a wannan mako zayyi bitar gasar motsa-jiki na zaratan da ke kare dajin daga farauta da kiwo ko sarar itatuwa wanda ake kira da Wildlife Ranger Challenge a Turance....more10minPlay
October 24, 2022Yadda bikin bayar da kyautar gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or ya gudana a ParisShirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda bikin bayar da kyautukan gwarzon dan kwallo ta Ballon d'Or ya gudana a birnin Paris, kyautar da a wannan shekara dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da Real Madrid Karim Benzema ya lashe saboda rawar da ya taka wajen taimakawa kungiyarsa kai labari a mabanbantan gasa cikin kakar da ta gabata. Ayi saurare Lafiya....more10minPlay
October 17, 2022Waiwaye kan rawar da Najeriya ta taka a gasar Commonwealth a BirtaniyaShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya tattauna ne akan irin rawar da tawagar 'yan wasan Najeriya ta taka a lokacin gasar guje-guje da tsalle-tsalle na kungiyar kasashe renon kasar Ingila wato Commonwealth da aka gudanar a birnin Birmingham ta kasar Birtania....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 206 episodes available.