Sign up to save your podcastsEmail addressPasswordRegisterOrContinue with GoogleAlready have an account? Log in here.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.... more
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 214 episodes available.
September 11, 2023Kungiyoyin kwallon kafa na ci gaba da shirin tunkarar gasar Primiyar NajeriyaShirin duniyar wasanni na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin kwallon kafa na arewacin Najeriya suka fara buga wasannin share fagen tunkarar gasar Primiyar kasar na bana....more10minPlay
September 04, 2023Yadda aka hada kungiyoyi a gasar zakarun nahiyar TuraiA dai ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar shirya wasan kwallon kafar nahiyar Turai UEFA ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai na bana, jadawalin da ke kunshe da kungiyoyi 32 wadanda aka karkasa zuwa rukunnai 8 wato kungiyoyi 4 a duk rukuni guda....more10minPlay
August 28, 2023Yadda magoya baya ke haddasawa kungiyoyi koma baya a Firimiyar NajeriyaShirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba kan yadda a wasu lokuta magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya ke janyowa kungiyoyin da su ke goyawa baya gagarumar koma baya a wasu lokutan har da tara ko zaftare maki....more10minPlay
August 21, 2023Yadda aka kaya a gasar cin kofin duniya ta mata 2023Shirin a wannan makon na musamman ne wanda ya yi duba gameda gasar lashe kofin duniya ta mata da aka kammala.Wannan ne karo na farko da kasashe biyu suka karbi bakuncin gasar lashe kofin duniya ta mata, kuma aka kara yawan kasashen da ke halartar gasar daga kasashe 24 zuwa 32....more10minPlay
August 14, 2023Duniyar wasanni na wannan mako zai duba gasar Kwallon kafar kasar Ingilayanzu haka dai an shiga rana ta 3 da soma gudanar da gasar wasannin kwallon kafar kasar Ingilia (premier Ligue) tare da Khamis Saleh wanda ya tattauna da masu ruwa da tsaki ta fanin kwallon kafa a Igila da Najeriya....more10minPlay
August 07, 2023Gasar kofin duniya ta mata ta dauki hankulan manazarta wasanniShirin Duniyar Wasanni' ma wannnan mako ya mayar da hankali ne kacoka a kan gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya inda yanzu haka ta kai matakin sili daya kwale. A halin da ake ciki, tawagar kasashe da dama dai sun koma gida sakamakon cire su da aka yi. Fitattaau daga cikin su sune, tawagar kwallon kafar Jamus da Brazil. Shirin ya duba yadda gasar ke tafiya da yadda manazarta wasan kwallon kafa ke kallonta....more11minPlay
July 17, 2023Shirin tunkarar gasar cin kofin Duniya ta Mata a Australia da New ZealandShirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh, a wannan makon ya mayar da hankali ne kan shirye-shiryen gasar lashe kofin duniya ta Mata da kasashen Australia da New Zealand za su karbi bakunci....more10minPlay
July 10, 2023Dawowar Kano Pillars da Katsina United gasar firimiyar NajeriyaShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan mako ya mai da hankali ne kan batun nasarar dawowa gasar Firimiyar Najeriya da kungiyoyin Kano Pillars da Katsina United suka samu a karshen makon jiya. Kamar yadda aka sani ne dai dukkanin kungiyoyin biyu wato Kano Pillars da Katsina United sun rikito zuwa aji na biyu ne a gasar ta Firimiyar da ta gabata, bayan gaza tabuka abun azo agani, abunda yasa suka karkare a ajin ‘yan dagaji....more10minPlay
July 03, 2023Gasar UEFA Nations League na kara samun karbuwa a duniyaShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon zayyi nazari ne akan gasar lik din da hukumar kulada kwallon kafar Turai UEFA ta samar, wacce ake kira da ‘UEFA Nations League’ kuma ana bugata ta ne lokacin hutun bazara don ta maye gurbin wasannin sada zumuncin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke shiryawa a irin wannan lokaci, amma kuma wasannin gasar basa shafar wasannin sharan fagen zuwa gasar lashe kofin duniya ko kuma na gasar Turai....more10minPlay
June 26, 2023Yadda lik din Saudiya ke kokarin dauko manyan 'yan wasan daga TuraiShirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon ya yi nazari ne akan yadda gasar lik din kasar Saudiya da ake kira da ‘Saudi Pro League’ ke kokarin dauko manyan ‘yan wasan kwallon kafa daga Turai musamman ma daga gasar Firimiyar Ingila. A farkon wannan wannan shekarar ce dai kungiyoyin da ke wannan gasa suka tashi tsaye wajen ganin sun kawo manyan ‘yan wasan kwallon kafa, duk tsadar su kuwa don su farfado da gasar da kuma samar mata da kima a idon duniya....more10minPlay
FAQs about Wasanni:How many episodes does Wasanni have?The podcast currently has 214 episodes available.