Wasanni

Wasanni

By RFI Hausa
Download on the App Store

Wasanni episodes

  • Senegal ta lashe gasar AFCON karo na biyu bayan nasarar da ta samu kan Morocco

    A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin.

    Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bai wa Morocco, lamarin da ya fusata ƴan wasan Senegal ficewa daga fili, amma daga baya Sadio Mane ya dawo da su aka ci gaba da fafatawa.

    Ɗan wasan gaba na Senegal Sadio Mane ne ya lashe gwarzon ɗan wasa a wannan gasa, Yassine Bounou na Morocco ya lashe gwarzon mai tsaron raga shima abokin wasansa Brahim Diaz da ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida ya lashe kyautar takalmin zinari da kwallaye 5.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

    10 min
  • An kammala gasar kokowa ta ƙasa mafi girma a Jamhuriyyar Nijar

    Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda aka kammala gasar kokuwar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar.

    Jiya Lahadi ne aka kammala gasar kokowar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a garin Tawa, wacce ita ce karo ta 46, inda mai masaukin baki ta lashe takobin bayan ƴan kokowarta biyu sun kai wasan ƙarshe a wannan gasa.

    Bayan karawa ta mintuna 11 da daƙiƙu 6, Nura Hassan ne ya yi nasara kan Zakiru Zakari.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Yadda aka yi bikin buɗe gasar cin kofin Afrika ta AFCON a Morocco

    Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zay yi duba ne kan yadda aka faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci.

    A daren jiya lahadi ne dai aka buɗe gasar lashe ƙofin nahigar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci.

    An dai buga wasanni tsakanin Morocco da Comoros, inda Moroccon ta samu nasasara da ci 2 da nema, wani abu da ke nuna cewa  ta faro gasar da ƙafar dama, bayan da Yariya Moulay Hassan bin Mohammed ya buɗe ta tare da rakiyar shugaban hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA Gianni Infantio da kuma shugaban hukumar kwallon ƙafar Afrika CAF Patrice Motsepe.

    Ɗan wasan gaba na tawagar Morocco Brahim Diaz da ke bugawa Real Madrid ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 55, kafin Ayoub El Kaabi na ƙungiyar Olympiacos da ya shigo daga baya ya ƙara a minti na 74.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Taƙaitaccen tarihi kan yadda aka faro gasar AFCON a shekarar 1957

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan tarihin gasar lashe kofin Afrika AFCON da hukumar CAF ke shiryawa.

    An faro buga gasar lashe kofin nahiyar Afirka, wacce ke zaman gasar kwallon ƙafa mafi girma da daraja a nahiyar a shekarar 1957, da hukumar kula da kwallon ƙafar Afrika CAF ce ta jagoranci.

    An fara gudanar da gasar ne a watan Fabrairun shekarar 1957 a birnin Khartoum na ƙasar Sudan da ƙasashe 3, kafin a shekarar 2019 aka faɗaɗata zuwa tawogogun ƙasashe 24, kuma Masar ce ta fara lasheta bayan lallasa Sudan da ta karbi baƙunci a wasan karshe, inda ta lashe kofin da aka sanya masa sunan Abdel Aziz Abdallah Salem, ɗan ƙasar Masar da ya fara shugabantar hukumar CAF.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Yadda aka gudanar da jadawalin gasar cin kofin duniya ta 2026

    Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda rabon jadawalin gasar lashe kofin duniya da za a yi a baɗi ya gudana.

    A makon da ya gabata ne Hukumar Kula da Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ta fidda jadawalin Gasar Kofin Duniya na shekarar 2026, wacce za ta gudana a tsakanin ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Bikin dai ya gudana a cibiyar Kennedy da ke birnin Washington DC, ƙarƙashin jagorancin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban FIFA Gianni Infantino.

    11 min
  • Matsalar da hukuncin ɗauke wasan Kano Pillars da Katsina Utd a gida ya ja musu

    Shirin awannan mako zai duba batun hukuncin ɗauke ƙungiyoyin Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin sun a gida a gasar NPFL ta Najeriya, da hukumar da ke shirya gasar ta yi.

    Kamar yadda masu bibiyar gasar Firimiyar Najeriya suka sani ne a baya bayannan, Hukumar Shirya Gasar NPFL ta Najeriya ta ɗauki hukuncin dakatar da manyan ƙungiyoyin arewacin Najeriya biyu wato Kano Pillars da Katsina United daga buga wasannin su na gida, inda aka maida Pillars buga wasan ta a Jihar Katsina, yayin da ita kuma Katsina United aka mayar da ita buga wasannin ta a jihar Pilato.

    11 min
  • Yadda Ashraf Hakimi ya lashe gwarzon shekara na Afrika karon farko

    Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafan Afirka da Achraf Hakimi na Morocco ya lashe.

    A makon daya gabata ne Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF, ta bayar da kyautuka ga zaratan ƴan wasan nahiyar da suka nuna bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita.

    A yayin bikin da ya gudana a birnin Rabat na ƙasar Morocco, hukumar ta CAF ta sanar da ɗan wasan baya na tawagar ƙasar ta Morocco wanda kuma ya ke yi wa ƙungiyar PSG wasa Achraf Hakimi,  a matsayin wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a wannan shekarar.

    Hakimi ya samu nasarar ce bayan doke shahararrun ƴan wasan nahiyar da suka taɓa lashe kyautar irinsu Mohamed Salah na Masar da ke taka leda a Liverpool,  da kuma Victor Osimhen na Nigeria da ke wasa a Galatasaray.

    Wannan ne dai karo na farko da ɗan wasan ya taɓa lashe ƙyautar, bayan da a karo biyu a jere ya na ƙarewa a mataki na biyu, a shekarar 2023 da Victor Osimhen ya lashe da kuma 2024 da Ademola Lookman ya lashe.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    10 min
  • Yadda ta kaya a karawar da aka yi tsakanin Najeriya da DR Congo

    Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda wasan ƙarshe na nemon gurbin wakiltar Afrika a matakin duniya, wajen samun tikin zuwa gasar lashe kofin duniya ya gudana tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Dimukaraɗiyyar Congo. Karawar da suka yi a filin wasa na Moulay Abdellah da ke birnin Rabat, ta kai matakin dugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da suka tashi 1-1.  

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............

    10 min

About Wasanni

From the publisher's feed

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

More shows like Wasanni

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners