
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48.
A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai kare kambun gasar ta yi waje da Switzerland.
Hankula sun karkata ga wasannin ƴan huɗu da suka rage a wannan gasa don ganin waɗanda zasu kai wasan ƙarshe.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya.
A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa.
Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32 suka yi saura.
Nahiyar Afrika da ke da wakilcin ƙasashe 10, 9 daga cikin su sun samu nasarar kaiwa wannan zagaye, waɗanda suka haɗa da Afrika ta kudu da Senegal da Morocco da Ghana Ivory Coast da DR Congo da Algeria da Masar da kuma Cape Varde, inda Tunisia ta yi adabo da gasar.
Shirin a wannan mako zai yi duba ne kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a gasar lashe kofin duniya ciki har da karawar da Cote d’Ivoire ta sha kashi a hannun Jamus.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu.
Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi baƙunci a shekarar 2022, jumullar ƙsashe 80 ne suka taɓa fafatawa a cikinta, inda aka buga wasan ƙarshe har 22 sai kuma ƙasashe 8 ne kawai suka taɓa lashe ta, inda Brazil ke da 5, Argentina da ke rike da kofin na da 4, Jamus da Italiya na da 3-3 sai Faransa da Uruguay da ta fara karɓar baƙuncin gasar ke da 2-2, yayinda Ingila da Spain kowaccensu ta lashe so guda-guda.
Ku latsa alamar sauti don sauaron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.............
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1.
Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a matsayin zakarar gasar, bayan tashi 1-1 da aka yi a karawar da akayi tsakanin Manchester City da Bournemouth.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh....................
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa.
A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila ce ake dakon jirar ƙungiyar da za ta lashe tsakanin Arsenal da Manchester City, waɗanda kowaccensu ke da ragowar wasanni biyu-biyu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya.
An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccensu za ta haska a gasar Firimiyar Najeriya a kakar baɗi.
A wasannin ƙarshe da aka aka yi, Sporting Lagos ta sha kashi da ci ɗaya mai banshi a hannun Inter Lagos, amma sai dai hakan bai hanata lashi gasar ba da ban-bancin ƙwallaye, domin kowaccensu ta ƙare ne da maki 6.
Wannan ne karo na farko da Sporting Lagos ta taɓa lashe kofin tun bayan samar da ita a shekarar 2022.
From the publisher's feed
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners