
Sign up to save your podcasts
Or


A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana gwagwarmaya a gasar firimiyar ƙasar wato NPFL.
Ƙungiyar ta shahara wajen horas da matasan ƴan wasa daga Arewacin Najeriya da kuma fafatawa da manyan ƙungiyoyi a ƙasar. A baya dai ƙungiyar ta Jigawa Golden Stars duk da namijin ƙoƙari da ta ke yi, ta taɓa shafe kusan shekaru bakwai ba tare da zuwa gasar Firimiyar Najeriya, kafin daga bisani ta sake komawa babbar gasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba.
Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na huɗu, saboda gajeruwar tazarar da ke tsakani, haka kuma abun yake a matakin ƙasan tebur inda nan ma ƙungiyar Wikki ce kadai kawo yanzu ake ganin da wahala ta tsallake, ya yinda ƙungiyoyin da ke mataki na 11 har zuwa matakin 19 kowaccen su bata da tabbas.
A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saley ya yi duba akan dambarwar da da ta taso dangane hukuncin karɓe nasarar Senegal ta lashe kofin Afrika na baya bayan da hukumar CAF tayi tare da maida nasarar ga ƙasar Morocco
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa.
Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda Amurka ta fara gargaɗin ƴan Ghana da ke da aniyar maƙalewa idan suka je ƙasar don kallon gasar cin kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci a watan Yuni mai zuwa.
Ganin irin matakan da dama gwamnatin Amurka ke ɗauka kan shigar baki ƙasar tuni ofishin Jakadancin ƙasar da ke Ghana ya fara gargaɗin masu shirin halartar gasar da su guji wuce wa’adin da aka basu.
Jakadan Amurka a Ghana Rolf Olson ya ce saɓawa dokokin shige da fice na ƙasar na iya haifar da mummunan sakamako, gami da rashin sake samun damar shiga ƙasar a nan gaba.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............
Shirin “Duniyar Wasanni” tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda aka sanya tsarin koyar da wasan kwallon ƙafa a makarantun Boko na Jamhuriyar Nijar.
A wannan makon mun yi dubi ne kan shirin koyar da wasan kwallon ƙafa da za a sirka a tsarin koyarwa a makarantun Boko a Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin da ake yi na haɓɓaka harkar, ganin yanda take a baya sosai a jadawalin ƙasashe da hukumar kwallon ƙafa ta duniya FIFA ta fitar inda Nijar ɗin ta ke a mataki na 111.
Shi dai wannan tsarin, ya kasance wani shiri ne na haɗin gwiwa da aka yi tsakanin hukumar FIFA da kuma gwamnatin Nijar wanda hukumar kwallon kafa ta ƙasar fenifoot ke kula da shi.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a garin Daura da ke jihar Katsina da ke a arewacin Najeriya.
A farkon watan Faburairun wannan shekarar ne aka kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da ƙungiyar sukuwar dawaki ta Najeriya ke shiryawa.
Wannan ne dai karo na uku da ake gudanar da irin wannan sukuwa a cikin wannan shekarar, bayan da aka yi ta farko a birnin Katsina sai garin Hadeja na jihar Jigawa ya karbi bakunci sannan aka kamma sukuwan zangon farko na wannan shekarar a Daura.
Mahaya daga Jihohin Kano da Sokoto da Neja da Bauchi da Kebbi da Katsina, waɗansu daga Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Mali da Chadi da kuma Burkina Faso, suka halarci gasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako, ya mayar da hankali ne kan taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta arewacin Najeriya.
Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh...
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya.
From the publisher's feed
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners