Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

By RFI Hausa
Download on the App Store

Al'adun Gargajiya episodes

  • Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa

    Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo?

    Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar guza, sannan a ɗaura masa tsirkiya guda biyu ko uku.

    A cikin shekarun da suka gabata, manyan mawaƙa irinsu Rabi'u mai Gurmi Gumel da Rabe mai Gurmi Jibia sun zagaya duniya suna baje kolin wannan fasaha.

    Amma a yau, idan ka zagaya biranen ƙasar Hausa, da kyar kake jin sautin wannan kiɗa, maimakon haka, sautin kiɗan na’urorin zamani na matasa sune suka mamaye ko'ina.

    Duk da wannan ƙalubale, wasu mawaƙan zamanin na ƙoƙarin haɗa sautin gurmi da kiɗan zamani don janyo hankalin matasa da kuma kaucewa ɓacewar wannan muhimmin kiɗa na al'ada.

    10 min
  • Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna

    Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

    11 min
  • Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin.

    Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda dukkaninsu suka taimaka wajen fito da Al'adar Hausawa a fili.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    12 min
  • Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa

    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. 

    Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a cikin kowane irin hali don kare su. Wannan tsarin ne da ya samo sali tun zamani da ake yaƙe-yaƙe tsakanin masarautu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa...........

    11 min
  • Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya

    Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a yankunan arewacin Najeriya musamman a makarantu ko ɗalibai da kuma wasu sassan Jamhuriyar Nijar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman...........

    11 min
  • Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar.

    Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa daban-daban na duniya, inda alƙaluma suka nuna cewar a shekarar bara baƙi fiye da dubu 100 ne suka halarci bikin.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min
  • Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu

    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na Turai da kuma naɗin wasu sabbin muƙaman na sarauta da suka shafi sassan nahiyar.

    Daya daga cikin kalubalen da Hausawa mazauna Turai ke fuskanta, shi ne bacewar harshen Hausa da al’adu a tsakaninsu, sai dai a yayin ziyarar da ya kai wa Sarkin Hausawan Turai da ke birnin Paris Alhaji Surajo Jan Kaɗo, Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar, ya yi alkawarin farfaɗo da martabar harshen na Hausa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    11 min

About Al'adun Gargajiya

From the publisher's feed

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin…

More shows like Al'adun Gargajiya

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners