
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Al’adunmu na Gado a wannan karon ya tattauna ne a kan Maita da kuma Kambun Baka, domin fahimtar banbancinsu a bisa bayanan masana a ɓangaren al’ada da kuma Addini. Wasu na ɗaukar maita a matsayin tsubbu inda a lokuta da dama su kan gadar wa ƴaƴansu. Sai dai kuma wasu masanan, na cewa maita baiwa ce da Allah ya yi ma wasu daga cikin bayinsa musamman domin bayar da magani ga marasa lafiya.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman........
Wannan shiri zai mayar da hankali ne kan yadda zamani ke tasiri akan salon magana ko gagara gwari a tsakanin al'umar hausawa, musamman ma matasa masana da dattawa da suka jiya suka ga yau sun bayyana dalilai da suka sanya irin wannan salo na zance, wanda ke nuna ƙwarewar harshe ke neman ɓacewa a tsakanin al'uma da gudummawar da kowanne ɓangare ke bayarwa wajen disashewar wannan fiƙira ta harshe.
Shirin al'adun mu na Gado na wannan mako zai Dora kan ci gaban Muhawara a tsakanin Masana kan kwarewar waƙa a tsakanin mawaki Shata da kuma Rarara
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin, tare a Nasiru Sani
Shirin al’adu na wannan makon ya waiwayi al’adar waƙoƙin Hausa ne da kuma tasirin Mawaƙan da suke rera su waƙoƙin a fannonin rayuwa daban daban.
A baya bayan nan aka tafka muhawara tsakanin wasu masana guda biyu na Adabin Hausa wato Dakta Abdul-Shakur Yusuf Ishaq na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma Dakta Mu’azu Sa’adu Kudan na Jami’ar Sule Lamiɗo da ke Kafin Hausa a jihar Jigawa, waɗanda suka baje iliminsu a kan matakin shahara, da kamance-ceniya da kuma banbanci a tsakanin Marigayi Mamman Ibrahim Yero da aka fi sani da Mamman Shata ko kuma Shata mai Ganga da kuma Dauda Adamu Kahutu Rarara da a halin yanzu zamani ke tafiya da shi.
Shirin a wannan makon zai tattauna ne a kan Camfi, da kuma yadda ya kasance a zamanin kaka da kakanni, da rawar da ya taka a waccan lokaci da kuma yadda yake shafar rayuwar jama’a a lokacin da muke.
Duk da ƙarancin lokaci, shirin Al’adunmu na gado zai yi ƙoƙarin zayyana rabe-raben al’adar ta Camfi ko kuma wasu daga ciki.
Shirin al'adunmu na gado tare da Oumarou Sani a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adun ƙabilar Dagomba a ƙasar Ghana, ƙabilar da ke ci gaba da mamaya a wannan ƙasa ta yammacin Afirka suk da kasancewarta wadda a baya tafi ƙarfi a yankin arewacin ƙasar.
Yanayin suturun wannan ƙabila na daga cikin abin da ke jan hankalin jama'a, musamman yanayin hularsu wadda ke da nufin ko kuma ma'anar zaman lafiya.
Suturun wannan ƙabila dai akan saƙa su da hannu ne.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A yau shirin zai mayar da hankali ne akan al'adar 'Dalilin Aure' a ƙasar Hausa da yadda aka zamanantar da ita.
A baya masu 'Dalilin Aure' a boye suke a cikin al'umma, sai dai yanzu a iya cewa zamani riga, domin kuwa za ka iske sun bude ofisoshi tare da sanya alamar cewa anan fa Dalilin aure ake.
Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan al'adar nan ta dalilin aure, guda cikin al'adun Hausawa da aka shafe tsawon lokaci ana amfani da ita da nufin haɗin aure walau tsakanin ƴammata da Samari ko kuma Zawara.
Kamar yadda kusan kowanne lamari ke tafiya da zamani itama al'adar ta juye, ta yadda ta koma cikakkiyar sana'a da wasu ɗaiɗaikun mutane ke da gogewa akanta, har ta kai ga ake buɗe ofisoshi don gudanar da ita.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Kamar yadda aka saba, shirin yakan yi dduba ne akan al'adun al'ummar Hausawa da sauran su, waɗanda suka gushe ko kuma ake ganin wanzuwan su a yanzu.
Al'adar tashe dai na daga cikin al'adun da aka fara ganin yaɗuwarsu a ƙasar Hausa tun a ƙarni na 16, al'ada ce da ta ƙunshi wasannin barkwanci, waɗanda ake gudanar da su da zarar a kammala azumin goman farko na watan Ramadana. Sai dai wannan al'ada ta fara gushewa. Ko menene dalilin haka? Abin da shirin wannan makon zai yi nazari a kai kenan.
shirin Al'adun Mu na Gado na wanan makon tareda Abdoulaye Issa ya leka Jihar Maradin Jamhuriyar Nijar inda al’adar aikin kwado da lizzami da aka share shekaru ana yin sa da hannu ke fuskantar barazanar samun babban koma baya sakamakon wasu sabbin na’urori ko teloli na zamani da aka samu masu aiki da Computer wadanda ke zuba wannan aiki ga riguna cikin gaggawa.
Ku shiga cikin alamar sauti domin sauraron shirin....
From the publisher's feed
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners