Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

By RFI Hausa
Download on the App Store

Al'adun Gargajiya episodes

  • UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na al’adun duniya

    Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, na sanya hawan Dabar Kano a arewacin Najeriya cikin kundinta na al’adun duniya.
    Bincike ya nuna cewar an fara gudanar da al’adar hawa Daba a lokutan bikin ƙaramar Sallah da Babba tun kafin jihadin Shehu Usman Dan fodio zamanin Sarkin Kano Rumfa.
     

    Masana a fannin tarihi sun ce zamanin Sarkin Kano Abbas, ya yi wa tsarin sauye-sauye wanda akan sa ake tafiya har zuwa wannan lokaci.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

    11 min
  • Gushewar al'adar tatsuniya a cikin al'ummar Hausawa

    Shirin 'Al'adunmu na Gado' na wannan makon tare da Abdoulaye Issa ya tattauna dangene da gushewar a'adar tatsuniya wadda ke zama hanyar da al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen  ilmantarwa, fadakarwa da kuma tarbiyantar da yara ta hanyar shirya kagaggun labarai masu kunshe da darussa.

    11 min
  • Masarautar Keffi a cikin shirin Al'adun mu

    Yau shekaru tara kenan da zama Sarkin masarautar keffi da mai martaba Dr alhaji shehu usman chindo yamusa,bayan      rasuwar mahaifinsa mai martaba alhaji Chindo Yamusa na uku 3.

    A cikin shirin al'adu za ku ji tarihin Sarkin na Keffi.

    10 min
  • Tasirin al'adun gargajiya wajen tafiyar da mulki bayan ficewar turawa

    Shirin al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa kamar yadda ya saba a wannan makon ma ya leƙo wasu daga cikin masarautun Hausawa don jin tarihi da kuma tasirinsu ga al'umma.

    A wannan karon shirin ya yi duba kan tasirin al'adun gargajiya a matsayin jigon tafiyar da shugabanci bayan ficewar turawan Mulkin mallaka a Najeriya.

    Haka zalika za kuji hira ta musamman da sarkin Keffi a jihar Nassarawa wato Mai martaba  Alhaji Shehu Usman Shindo Yamusa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.....

    11 min
  • Yadda bikin baje kolin cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery da ke Lagos ya gudana

    Shirin al'adunmu na gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda aka gudanar da gagarumin biki baje kolin al'adu a jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya. An gudanar da bikin ne a fitacciyar cibiyar al'adu ta Nike Art Gallery, wanda ya shahara a duniya, bikin ya tattaro mutane da dama daga sassan fasaha, kasuwanci, siyasa da diflomasiyya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Aboulaye Issa........

    10 min
  • Sarkin Damagaram ya naɗa ɗan Najeriya a matsayin Talban masarautarsa

    Shirin Al'adu na wannan makon ya duba irin yanda masarautunmu na gargajiya ke kama hanyar zama ƙasa da ƙasa ta yanda sarakunan wasu masarautun ke nada ƴan wasu ƙasashe don basu mukamin a fadodinsu da sunan ƙarfafa zumunci da kyautata rayuwar jama'ar ƙasashen. A baya-bayan nan, mai Martaba Sarkin Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar ya naɗa Alhaji Idriss Ousmane Kwado, a matsayin Talban Damagaram, bikin ya samu halartar gwamnonin jahar Zinder da na Katsina da wasu manyan sarakunan Arewacin Nigeria. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......

    10 min
  • Yadda aka gudanar da bikin Sallar Gani a Najeriya da Nijar

    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon yayi duba ne kan yadda ake gudanar da bikin Sallar Gani. ita dai wannan sallar na daga cikin dadadun al’adar mallam Bahaushe, kuma har yanzu ana gudanar da wannan biki a  wasu masarautu a Arewacin Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.......

    11 min
  • Shirye-shirye na musamman kan tarihin zuwan Turawa ƙasar Hausa

    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ci gaba ne game da jerin shirye-shiryen da muka faro kan zuwan Turawan mulkin mallaka zuwa ƙasar Hausa. Turawan sha mamakin abinda suka tarar, kasancewar sun samu al’ummar Hausawa da cikakkiyar wayewar addini, sarauta, sutura, karatu da rubutu da kuma wayewar kasuwanci da sauran harkoki na rayuwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare ta Abdoulaye Issa.......

    10 min

About Al'adun Gargajiya

From the publisher's feed

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin…

More shows like Al'adun Gargajiya

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners