Al'adun Gargajiya

Al'adun Gargajiya

By RFI Hausa
Download on the App Store

Al'adun Gargajiya episodes

  • Dawowar tsafe-tsafe a tsakanin al'umma kashi na biyu

    Shirin Al’adun Mu na Gado a wannan makon ya kawo muku ci gaban tattaunawa da Dakta Tahir da ake kira da Babba Impossible, wanda a makon daya gabata ya fara fashin baƙi a lamarin da yashafi tsafe-tsafe. Haka nan shirin ya leka Jamhuriyar Benin, inda gwamnatin ƙasar ta sanar da rusa wasu masarautu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa............

    10 min
  • Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga  ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja.

    Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    11 min
  • Yadda tsamin alaƙar gwamnati da Sarakuna ke raunata Masarautun gargajiya

    Shirin 'Al'adunmu na Gado' tare da Abdoulaye Issa a yau mayar da hankali kan rashin jituwar dake faruwa tsakanin gwamnoni a Najeriya da kuma ɓangaren Sarakunan gargajiya wanda har takai ga wasu jihohin na rushe Masarautu suna kuma kirkirar sababbi.

    A ‘yan shekarun nan, an sami irin wanann takun saka a jihohi irin Kano da Sokoto da Adamawa da kuma Katsina dukkaninsu a sassan Arewacin Najeriyar, inda masana tarihi da al’adu ke kallon al’amarin a matsayin barazana ga tsarin Sarautar mai dogon tarihi.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

    10 min
  • Ƴan China da ke Najeriya sun gudanar da bikin sabuwar shekararsu

    Shirin Al’adun mu na gado na wannan makon ya mayar da hankali ne ga bukuwan sabuwwar shekara na ƴan ƙasar China, bukukuwan da aka gudanar  a sassa daban daban na duniyar. A Najeriya, ƴan China ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen gudanar da wannan biki a biranen Abuja da kuma Lagas, wanda ya samu halarta  jama’a baki daga ciki da waje.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa.........

    10 min
  • Yadda al'adar shaɗi ko kuma Charo ke gudana tsakanin al'ummar fulani a baya

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ke kan al'adar shaɗi ko kuma Charo na sahun manyan al'adun ƙabilar fulani a ƙasashen Afrika ta yadda har sai wanda ya iya karɓaɓɓen shaɗi ke iya samun matar aure, yayinda a wasu lokutan ake gudanar da wannan al'adu a shagulgula don nishaɗi kuma jajirtacce shi ne jarumi.

    10 min
  • Yadda Hausawa ke ƙoƙarin yin watsi da al'adar amfani da kwarya

    Shirin Al'adun mu na Gado a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa ke ƙoƙarin mancewa da al'adar amfani da kwarya, wacce ke cikin daɗaɗɗun kayan amfanin gida na Malam Bahaushe. To sai dai duk da irin tasirin Kwarya a cikin al’ummar ta Hausawa, sannu a hankalin wannan al’ada tana neman gushewa a tsakanin al’ummar ta Hausawa har ma da Fulani da suka rungumi al’adar daga baya.

    Masu harkar sayar da ƙore a yankin Arewacin Nigeria, na kokawa sosai kan rashin garawar sana’ar tasu sakamakon yadda Hausawa da Fulani suka rage amfani da Kwarya.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Abdoulaye Issa........

    10 min

About Al'adun Gargajiya

From the publisher's feed

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam.  Akwai kuma Shirin…

More shows like Al'adun Gargajiya

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners