
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.
Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka.
Cibiyar ta ce adaɗin ya zarce jimillar kuɗin da aka ware wa manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya guda bakwai. Batu da ya janyo ce-ce-ku-ce.
A cikin rahotonta, Cibiyar ta nuna cewa gwamnatin ta ware kusan Naira biliyan 960 ga ma'aikatun Sufurin Jiragen Sama, Gidaje, Harkokin Mata, Ciniki da Masana'antu, Shari'a, Kiwon Dabbobi da Albarkatun Man Fetur, amma kuma ta ware kusan Naira biliyan 963 domin sayen motoci da kuma ayyukan tallafa wa jama'a.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira.
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi karɓar bashin kiran waya daga kamfanonin sadarwa, inda a bara kaɗai wani rahoto ke cewa jama'ar ƙasar ta yammacin Afrika sun ci bashin kiran wayar da ya kai naira tiriliyan 4 da biliyan 61.
Shirin ya nazarci tasirin hada-hadar kuɗaɗen da ake kashewa a fannin sadarwa inda ya ke a bayyane yadda kamfanonin sadarwa ke samun tarin kuɗaɗen ruwa daga basukan da ƴan Najeriyar ke ci, wanda ya ƙaru da fiye da kashi 10.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61.
Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna yadda ƴan Najeriya waɗanda ke amfani da wayar hannu, a kullum ke tururuwar ciwo bashin katin kira wanda ke ɗauke da kuɗin ruwa.
Rahoton cibiyar ya ce a shekarar 2025 kawai ƴan Najeriya sun ci bashin katin kiran waya da ya kai Dala biliyan 3 da miliyan 18 kwatankwacin Naira tiriliyan 4 da biliyan 61, abinda ke haskawa ƙarara cewa adadin ya ƙaru da kaso 12.3 cikin 100 idan an kwatanta da shekarar 2024, wadda ya kasance Naira tiriliyan 4 da biliyan 38.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali.
Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu.
Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyarsu na sake jifasu cikin damuwa.
A cikin 'yan watannin nan, koke-koke sun mamaye kafofin sada zumunta, sakamakon rashin karin bayani kan yawaitan kudaden da bankunan ke cirewa..
Duk da cewa bankuna sun dage cewa hakan tsari ne da kuma sahalewar haka daga babban bankin kasar CBN, kwastomi na diga ayar tambaya kan cirewa fiye sau ɗaya kan, ko kuma daga wanda ya tura da kuma wanda ya ƙarba, yayin da wasu ke kokawa kan rashin maida musu kudinsu nan take idan aka samu masalar sabis kudi bai je ga wanda aka tura ba da dai sauransu...
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu .
Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu .
Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsadar sufuri.
‘Yan kasuwa, na kukan samun wagegen gibi tsakanin uwar kudin jarinsu da abinda suke kashewa na safarar kayansu zuwa kasuwanni, saboda tsadar kudin sufuri da kuma rashin ciniki saboda halin rashin kudi da ‘yan kasar ke ciki.
Kasancewar kowane sasshen Nigeria na da nau’in kayayyakin da yake da su a wadace, ‘yan kasuwa daga arewacin kasar, kan saro kayayyaki irin su Manja da Man Gyada da Garin Kwaki da makamantan su, daga kudancin kasar, yayinda ‘yan kasuwa daga kudanci, kan sayi hatsi, dabbobi da makamantan su daga arewacin kasar.
Bayanan hukumar kididdiga ta Nigeria, sun yi nuni da cewa damar ikon sayen kayayyaki a kasuwanni wato purchasing power a turance, da ‘yan Nigeria ke da ita, ta ragu da kashi 21, a sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyakin suka yi, da koma-bayan kudin shigar masu karamin karfi a kasar.
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru.
Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners