
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta’addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta. A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi’a.
Wannan mataki ba iya Najeriya ta shafa ba, harma da ƙasashen Burkina Faso da Afrika ta Kudu da ma Mozambique duk a nahiyar Afrika.
Cibiyar wadda ke da hedikwata a birnin Paris na ƙasar Faransa, wadda ke gudanar da binciken kwakwaf kan yadda ake hada-hadar kuɗaɗe tsakananin ma’aikatun gwamnati da hukumomi ko kuma cibiyoyin gwamnati ta ce duk da cire waɗannan ƙasahe cikin baƙin littafinta, har yanzu za’a ci gaba da sanya idanu akan waɗannan ƙasashe.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba................
A wannan makon shirin na 'Kasuwa Akai Miki Dole' tare Ahmed Abba zai tattauna ne kan taron ƙoli na ƙasa da ƙasa domin bunƙasa zuba jari da harkokin kasuwanci na farko da jihar Bauchi da ke tarayyar Najeriya ta karɓi baƙunci. Ɗaya daga cikin matsaloli da ke nakasa ci gaban harkokin kasuwanci a Najeriya da sauran ƙasashe masu tasowa ita ce matsalar janyewar masu zuba jari daga fagen harkokin kasuwanci, saboda haka ne ma gwamnatin jihar Bauchi da ke yankin arewacin Najeriya ta shirya wannan taro kan zuba jari irin sa na farko a tarihi.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba.....................
A wannan makon shirin na Kasuwa Akai Miki Dole tare Abdulƙadir Haladu Kiyawa zai tattauna ne a kan yawaitar matasan Najeriya masu muhimman sana’o’in hannu da ke yin ƙaura ko kuma tafiya ci rani zuwa wasu ƙasashen Afrika domin neman na rufin asiri, abin da ake alaƙantawa da dalilai da dama da ke sanya matasan ficewa daga ƙasar tasu ta haihuwa.
A shekarun baya ba haka lamarin yake ba, inda Najeriyar ke matsayin wajen da ɗimbin ƴan ƙasashen ƙetare ke kwarara don neman kuɗi musamman ƴan kasashen Afrika kamar Jamhuriyar Nijar, da Ghana, da Jamhuriyar Benin, har ma da Kamaru.
To Sai dai a yanzu, waɗannan ƙasashen ne ƴan Najeriyar ke tururuwar zuwa cikinsu duk da kasancewar ƙasashen ba su da ɗinmbin arziƙi kamar Najeriyar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...
Shirin ‘Kasuwa A Kai Miki Dole’ na wannan mako zai tattauna ne kan wasu alƙaluma da suka nuna yadda Najeriya ta Kashe Dala Biliyan 2.86 a cikin watanni 8 na farkon shekarar da muke ciki ta 2025, wajen Biyan Kuɗin Ruwan Basukan da ta karɓo daga ƙasashen ƙetare tare da Nura Ado Suleiman.....
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin...........
Shirin kasuwa a Kai miki dole na wannan mako ya yi duba ne kan yadda ake gudanar da hada-hadar kayayyakin amfanin gona da ake samu a damina,waɗanda ake shukawa da sauran tsirrai da ake samu a daji saboda saukar ruwan sama.Ɗaya daga cikin falalar ruwa ita ce Allah ya rayar da amfanin gona.Da zarar damina ta yi nisa kayan amfanin gona da sauran tsirrai da ba shukasu aka yi ba, suka fara yabaya, to daga nan za’a fara ganin hada-hadar waɗannan kayayyaki irinsu ɗanyar masara,wake, gujiya,da wasu ƴaƴan itatuwa da ake samu a wannan lokaci kadai, harma halitu irinsu Fara.
Latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Ahmed Abba............
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya dubi batun ƙarin da aka samu a rabon arzikin ƙasa na wata-wata da gwamnatin Najeriya ke yi tsakaninta da jihohi da ƙananan hukumomin ƙasar, inda alƙaluma su ka nuna yadda wannan kaso ya ƙaru da ninkin abin da aka saba rabawa a baya, tun bayan zuwan wannan gwamnati ta shugaba Bola Tinubu a shekarar 2023.
Ɓangararorin gwamnatoci uku a Najeriya, wato ta tarayya da ta jihohi da kuma ƙananan hukumomi sun raba kaso mafi yawa a tarihin rabon tattalin arzikin ƙasa na wata wata wanda ya kai sama da Naira Tiriliyan 2 da biliyan 200 a watan Agustan da ya gabata....
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ake ƙara samun raguwar kayayyakin masrufi a Najeriya. Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, tace watanni biyar jere kenan, ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, inda tace an samu sauƙar farashin kayyaki a watan Agustan da ya wuce, da kaso 1 da ɗigo 76 cikin 100, wanda hakan ke nuna yadda aka samu sauƙi fiye da kaso 21.88 na watan Yuli, yayin da yanzu kuma ya koma kaso 20.12 cikin 100.
Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin Babban bankin Najeriya CBN da ya umarci bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su sanya na’urar bin diddigi ta taswira wato GPS a tashoshin POS a fadin ƙasar, a wani mataki na dakile ɓata gari a bangarori daban-daban masamman ma ayyukan ƴan damfara.
Latsa alamar sauti domin sauraaron cikakken shirin......
Shirin kasuwa akai miki Dole na wanan makon tare da Abdulkadir Haladu Kiyawa ya mayar da hankali ne kan yadda karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, ke ci gaba da haɓaka tattalin arziƙin ƙasashen da ke maƙwabtaka ita waɗanda ke amfani da kuɗin CFA.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, zai tattauna ne kan ƙalubalen da ake fuskanta na durƙushewar kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya, duk da zuba jarin dubban biliyoyin Naira da ‘yan kasuwa suka yi wajen kafa kamfanonin sarrafa shinkafar, waɗanda rahotanni suka tabbatar da cewa an rurrufe da dama daga cikin kamfanonin ko kuma an rage adadin shinkafar da su ke sarrafawa.
Wani bincike ya ƙiyasta cewa a shekarar 2018, Nigeria kan sayi shinkafar da ba ta gaza ta Nera triliyan 2 da rabi ba, yayin da kuma kusan kashi 90 na hada-hadar cinikin shinkafa da ake yi, na gudana ne ba a hukumance ba.
Alƙluma dai sun nuna Nigeria ke kan gaba a faɗin nahiyar Afrika wajen sayen shinkafa daga ƙasashen ƙetare, kamar yadda hukumar kula da hada-hadar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen na waje ta tabbatar, inda a duk shekara, ake shigar da shinkafa cikin Najeriyar ta zunzurutun kuɗi Nera Triliyan 9 da biliyan 200.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners