
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, zai tattauna ne kan ƙalubalen da ake fuskanta na durƙushewar kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya, duk da zuba jarin dubban biliyoyin Naira da ‘yan kasuwa suka yi wajen kafa kamfanonin sarrafa shinkafar, waɗanda rahotanni suka tabbatar da cewa an rurrufe da dama daga cikin kamfanonin ko kuma an rage adadin shinkafar da su ke sarrafawa.
Wani bincike ya ƙiyasta cewa a shekarar 2018, Nigeria kan sayi shinkafar da ba ta gaza ta Nera triliyan 2 da rabi ba, yayin da kuma kusan kashi 90 na hada-hadar cinikin shinkafa da ake yi, na gudana ne ba a hukumance ba.
Alƙluma dai sun nuna Nigeria ke kan gaba a faɗin nahiyar Afrika wajen sayen shinkafa daga ƙasashen ƙetare, kamar yadda hukumar kula da hada-hadar fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen na waje ta tabbatar, inda a duk shekara, ake shigar da shinkafa cikin Najeriyar ta zunzurutun kuɗi Nera Triliyan 9 da biliyan 200.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yunkurin da gwamnatin Najeriya Ke yi na ganin ta farfado da tattalin arzikinta, ta hanyar tada masana'antun da suka durƙushe. Ƙaramin ministan kasuwanci na ƙasar Sanata John Owan Enoh ya fara ziyarar wasu daga cikin masakun da suka durƙushe domin ganin sun dawo bakin aiki.
Masaka ta UNTL da Ke Kaduna na cikin masakun da ministan ya ziyarta bisa ganin irin gudummuwar da ta ke bayar wa a baya.
Ku latsa alamar sauti don saurorin cikakken shirin tare da Ahmed Abba............
To kamar yadda akaji a matashiyar shirin, ra’ayoyin masana tattalin arziki sun banbanta a Najeriya, tun bayan da sananne a harkar tattalin arziki Bismark Rewane ya tabbatar cewa Naira ta daidaita tsakanin 1500 zuwa 1560 kan kowace dala a makonnin baya-bayan nan, yayin da tattalin arzikin ƙasar kuwa ya fara farfadowa sakamakon matakin babban bankin na Najeriya CBN da ya sanya zunzurutun ƙudi har dalar Amurka biliyan 4 da miliyan 100 cikin watanni shida na wannan shekara...ta 2025.
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan sabuwar dokar Harajin da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu a ƙarshen watan Yunin wannan shekara ta 2025 a matsayin wata sabuwar dokar haraji da za ta taimaka wajen sake yi wa tsarin tattara harajin ƙasar garambawul kamar yadda su ka bayyana.
Sabuwar dokar ta kuma yi bayani dalla-dalla kan waɗanda za ta shafa tare da cire wasu nau'ukan ƴan Najeriya kama daga ƴan kasuwa da ma'aikata da ma manya da matsakaitan kamfanoni. Kuma domin sanin waɗanda da dokar ta bada damar karɓar haraji a wurinsu da ma waɗanda ta ce a ɗage musu tare da irin tasirin da za ta yi ga tattalin arziƙin ƙasar.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yau Shirin zai mayar da hankali ne kan ziyarar kwamitin shugaban Najeriya kan saukaka harkokin kasuwanci a jihohin arewa maso gabas.
Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba
Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Aisha Shehu Kabara a wannan makon, ya maida hankali ne kan taron koli na farko kan ƙarfafa ci gaban tattalin arzkin ƙasashen Afrika ta Yamma da aka gudanar a Najeriya, ta hanyar sauƙaƙa tsarin kasuwanci ga ƴan kasuwar da ke zirga-zirga a tsakani.
Ku lasha alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya yi duba ne kan girman asarar da al’ummar Makwa na jihar Naija suka tafka masamman ma ƴan kasuwarsu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa garin a ƙarshen watan Mayan wannan shekara ta 2025.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan wani sabon bashin da Najeriya ta ciwo daga bankin duniya da ya haura sama da dala biliyan ɗaya. Wannan sabon bashin dai ya janyo cece-kuce daga ƴan ƙasar waɗanda suka nuna damuwa kan yadda gwamnati ke ci gaba da ciyo manyan basussuka duk da iƙirarinta na janye tallafin manfetur domin dogaro da kai.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba............
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne kan babban taron da ƙungiyar Matan Arewa ƴan kasuwa mazauna Lagos da ke kudancin Najeriya su ka yi a birnin Lagos, wanda ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arzikinsu.
Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan makon tare da Ahmed Abba ya yi duba kan irin girman asarar da masau kamfanoni su kace sun tafka saka makon matsalar karancin wutan lantarki da ake fama da ita musamman a arewacin kasar.
Ku shiga alamar sauti domin jin cikakken shirin......
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners