Kasuwanci

Kasuwanci

By RFI HausaBusiness
Download on the App Store

Kasuwanci episodes

  • Yadda manoman zoɓo a Najeriya suka  fuskanci kalubale a harkar

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan halin da ake ciki game da noman zoɓo a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, da kuma yadda ake fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare. Duk da cewa ana noman zoɓo a Jihohi irin su Zamfara da Katsina da Kano da Kebbi da Borno da Yobe, bayanai na cewa kusan kaso 70 cikin 100 na zobon da ake fita da shi ƙasashen waje a jihar Jigawa ake nomawa, sai dai a shekaru biyu da suka gabata manoman na zoɓo sun ɗan  fuskanci kalubale a harkar.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........

    13 min
  • Ghana ta bai wa 'yan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare

    Yau shirin ya yada zango ne ƙasar Ghana, inda ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin ƙasar na bai wa ƴan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare.

    Ƙasar Ghana ta bai wa ƴan ƙasashen waje da su fice daga harkokinta na kasuwancin zinare a ƙarshen wannan wata na Afirilu a wani mataki na bunƙasa kananan masu hakar zinare na cikin gida da kuma samun ƙudin shiga.

    Ƙasar ta yammacin Afirka dake kan gaba a samar da zinare a nahiyar na ƙokarin tsaftace harkokin harƙar zinare ta hanyar daidaita cinikin zinari daga kananan masu hakar ma'adinai.

    10 min
  • Tasirin sabbin harajin Amurka ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin matakin shugaban Amurka Donald Trump kan shirin sa na sanya gagarumin ƙarin haraji ga kusan ɗaukacin ƙasashen duniya, wanda ya jawo durƙushewar kasuwannin  hannayen jari ta duniya da lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙawayenta, duk da cewa ya yi amai ya lashe wajen dakatar da harajin da watanni uku masu zuwa. Shirin ya duba tasirinsa ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya.

    11 min
  • Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya

    Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yi dubi ne kan halin da fannin kasuwanci ke ciki a Najeriya sakamakon barazana ko ƙoƙarin mamaya da ƴan ƙasar China ke yi, wanda aka tabbatar da irin illar da ayyukansu ke haifarwa ga ƴan kasuwa da kuma tattalin arziƙin ƙasar.

    Ba sabon abu bane yadda ake samun ƴan ƙasar China da ke aikata abubuwan rashin ɗa'a kama daga ɓangaren haƙar ma'adai ba bisa ƙa'ida ba, yin kutse ga ƴan kasuwa, zamba cikin aminci a intanet da sauransu.

    Sai dai ana zargin har izuwa yanzu, babu wani tsatsauran mataki na azo a gani da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wurin kawo ƙarshen irin waɗannan laifuffukan da ake samun ƴan ƙasar na yi a Najeriya. 

    Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

    11 min
  • Dalilan da suka sanya farfaɗowar darajar Naira a kasuwar musaya

    Shirin ‘Kasuwa a kai miki Dole’ tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan farfaɗowar darajar Naira a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, musamman ma a kan Dalar Amurka, nasarar da wasu ke ganin ta biyo bayan manufofin da babban bankin Najeriya CBN ke aiwatarwa.

    Bayanai dai sun nuna cewa darajar Naira na ta ƙaruwa ne kusan a kowace rana tun daga watan Janairun wannan shekara da mu ke ciki ta 2025. Nasarar da wasu Magidanta suka ce sun shaida samun ta, la’akari da sauƙin da aka fara samu a harkokinsu na yau da kullum.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

    10 min
  • Yadda ake samun sauƙin farashin kayayyakin masarufi a sassan Najeriya

    A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ake kara samun saukar farashin kayan masarufi a sassan Najeriya.

    Bayanai da muka tattaro na nuni da cewa yawancin kayayyakin da farashin su ya sauka na amfanin gona ne da kuma na kamfanonin kasashen waje, amma na kamfanonin cikin gida har yanzu suna nan a yadda suke.

    A makon jiya Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3.

    Cikin sanarwar da ta fitar a Talatar wancan makon, hukumar ta NBS ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriyar ya sauka ne zuwa kashi 24.4 a watan Janairun wannan shekara, saɓanin kashi 34.8 da aka gani a watan Disambar shekarar bara ta 2024.

    10 min

About Kasuwanci

From the publisher's feed

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

More shows like Kasuwanci

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners