Kasuwanci

Kasuwanci

By RFI HausaBusiness
Download on the App Store

Kasuwanci episodes

  • Yadda gwamnan CBN ya kashe naira biliyan 60 wajen siyen motocin alfarma

    Shirin "Kasuwa akai miki dole" tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin Babban Bankin Najeriya CBN na sayen motocin sulke na katsaita guda shida da ƙudin su ya haura naira biliyan 60, wanda gwamnan bankin da mataimakansa za su yi amfani da su, daidai lokacinda ƴan ƙasar ke fama da tsananin tsadar rayuwa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

    10 min
  • Tasirin da tsarin musayar zinare ga makamashi ya yi ga tattalin arzikin Ghana

    Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya waiwayi shirin  gwamnatin Ghana na ban gishiri in baka manda a musayar zinare da man fetir, duk dai a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na haɓaka tattalin arziƙinta.

    Tun a bara ne gwamnatin na Ghana ta ƙaddamar da tsarin na ban gishiri in baka manda, wanda ta ƙarbi tan dubu 40 na man disel da ƙudinsu ya kai dala miliyan 40 wajen musanya da zinare da ƙasar ke da arzikinsa.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...

    10 min
  • Masu sana'ar kifi a Najeriya sun koka kan tsadar abincin kiwo

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba yadda kasuwancin kifi a Najeriya ya ke neman ya gagari masu sana’ar saboda tsadar abincin da ake kiwon kifi da shi da farashin sa ya ƙaru, lamarin da ke barazana musamman ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa a fannin.

    Farashin buhun abincin kifi ya tashi daga N18,000 a shekarar 2023 zuwa N36,000 a wannan shekarar, wanda ya nuna karuwar kashi 100 cikin 100 a fadin Najeriya.

    Wannan al’amari ya yi kamari a yankin Neja Delta da suka yi kaurin suna a noman kifi.

    11 min
  • Najeriya ta yi asarar sama da naira triliyan 5 a zanga-zangar kwanaki 10

    Shirin Kasuwa A kai miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya tattauna irin asarar da aka yi a Najeriya sakamakon zanga zangar kwanaki 10 da ƴan ƙasar suka yi domin nuna adawa da tsadar rayuwa da rashin shugabanci na gari.

    Ministar masana’antu da Kasuwanci da kuma zuba jari na kasar Dr. Doris Uzoka Anite ta ce, alkakuma da suka tattara na wucin gadi, sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar naira biliyan 500 a duk rana ta Allah yayin zanga-zangar, bayaga dukiyar da aka barnata ta hanyar kone-kone ko sata da makamanci hakan da takai naira biliyan 52, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

    10 min
  • Yadda basuka su ka yi wa ƙasar Ghana katutu a cikin shekara guda

    A yau shirin zai waiwai kasar Ghana, inda basusukan da ake bin kasar ya karu da dala biliyan 47.4 / Cidi biliyan 658.6 a cikin watanni biyun farko na shekarar 2024.

    Babban Bankin ƙasar ta Ghana ne ya fitar da wadandan alkaluma cikin wani rahoton da ya fitar na taƙaitaccen Bayanan Tattalin Arziki da Kuɗi na watan Mayun shekarar 2024.

    A cewar babban bankin na Ghana, bashin da ake bin ƙasar ya karu ne zuwa Cidi biliyan 658.6 a watan Fabrairun wannan shekarar, tsabanin Cidi biliyan 611.2 da yake a ƙarshen shekarar 2023.

    10 min
  • Yadda Najeriya ke fuskantar tashin farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 30

    A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da hukumar ƙididigar ta Najeriya ta fitar cewa an sake samun hauhawan farashin kayayyaki wanda ƙasar ba ta taɓa gani ba cikin shekaru 30, daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke faɗi tashin kawowa al’umma sauƙi kan tsananin rayuwa da suke ciki, tare da amincewa da Naira dubu 70 a amatsayin mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

    Shin ko hakan zai kawo sauƙi kan halin da ake ciki a ƙasar? Kuna iya latsa alamar sauti don jin amsar wannan tambaya tare da masana ta cikin shirin...

    11 min
  • Gwamnatin Najeriya za ta yi odan abinci daga waje saboda tsadar rayuwa a ƙasar

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' a wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan sabon matakin gwamnatin Najeriya na sahale shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa da wake da alkama da masara ba tare da biyan ƙudin fito ba har tsawon watanni 5, domin rage tasirin tsaɗar kayan abinci da ƴan ƙasar ke fama da shi tun bayan ɗarewar shugaba Bola Ahmed Tinubu mulki a bara.

    A wani taron manema labarai da ya kira wannan Litinin, ministan noma da samar da abinci na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana sabon matakin, inda ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito da kuma haraji kan muhimman kayan abincin ne har na tsawon kwanaki 150, domin wadatuwar kayan a Najeriya.

    Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ƴan kasuwa masu bukatar shigo da kayan abinci, ita kanta gwamnatin tarayya za ta shigo da alkama da Masara kimanin tan dubu 250 kowanensu, domin bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.

    11 min
  • Yadda gwamnatin Nijar ta saukaka farashin shinkafa ga al'ummar kasar

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali kan yadda gwamnatin Jamhuriyar  Nijar, ta fara saidawa talaka shinkafa a farshi mai rahusa, domin saukakawa ƴan kasar radadin matsin tattalin da suke ciki sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi.

    A ranar 26 ga watan Yunin da ya gabata gwamnatin Nijar ta hannun ma’aikatar kasuwanci ta kaddamar da wannan shirin,  inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo 23 kan jaka 13 da rabi maimakon jika 17 zuwa jika 19 da ake sayar da shi a a wasu wurare.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

    10 min
  • Lokaci ya yi da Najeriya za ta rinka fitar da manja kasashen waje - Ƙungiyoyi

    Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali da kan kiranda wasu kungiyoyi suka yi wa gwamnatin Najeriya da ta yi wa Allah ta farfado da harkokin noma da sarrafa manja kamar yadda aka san ƙasar a baya. Kungiyar ɗalibai ta ƙasar ta yi  kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya farfado da harkokin sarrafa manja da Allah ya wadata ƙasar da shi, ta yadda hajar zata wadata ƴan Najeriya da ma fitar da shi ƙasashen waje kamar yadda lamarin yake a baya.

    Kirin ƙungiyar ta NANS na zuwa ne bayan da Shugaban ƙungiyar masu samar da manja ta Najeriya Mista Alphonsus Inyang, ya ce Najeriya na kashe sama da daka miliyan 600 duk shekara wajen shigo da Manja daga katare duk da cewa Allah ya albarkaci ƙasar da kwakwan Manja.

    Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

    10 min

About Kasuwanci

From the publisher's feed

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

More shows like Kasuwanci

Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Muhallinka Rayuwarka by RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners