
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wannan mako ya tattauna akan yadda faduwar darajar Naira ke haddasa koma bayan kasuwar 'yan canji a makwaftan Najeriya.
Shirin Kasuwa a Kai Maki Dole na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da batun wutar lantarki a Najeriya, bangaren da ke fama da matsalololi tsawon shekaru.
Shirin zai yi dubi ne a game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sokewa da kuma sabunta lasisi ga wasu kamfanonin da ke da alhaki rarraba wuta a cikin kasar.
Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wanna makon ya mayar da hankali akan faduwar darajar naira da ke ci gaba da yin illa ga harkokin kasuwanci a sassan Najeriya.
Wakilinmu a jihar Kano Abubakar Abdulkadir Dangambo ya duba yadda matsalar ke yin tasiri musamman babbar kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano, wadda ke tattara 'yan kasuwa daga Najeriya da kuma kasashe irin su Chadi da Kamaru da Nijar da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Shirin "Kasuwa akai Miki dole" na wanan mako tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Dosso dake Jamhuriya Nijar, yankin da ke kan iyaka da birnin Cotonou na Jamhuriya Benin inda jama'a suka shiga matsanancin halin tsadar rayuwa tare da kariyar tattalin arziki, sakamakon takun-kuman da Kungiyayoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka laftawa kasar, saboda Juyin mulkin da Sojoji sukayi.
A Ranar 9 ga Watan Octoba da ya wuce Jamhuriya Benin ta rufe iyakar dake tsakaninta da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, bayan matakin da Kungiya ECOWAS ko CEDEAO ta dauka bayan da sojoji suka karbe mulki Ranar 26 ga watan Yuli wajen hambarar da shugaban Mohamed Bazoum.
Jamhuriyar Bénin ta dauki matakin soke duk wata hulda cinikaya da gwamnatin sojin Nijar.
Wanan matakin dai ya janyo hauhawa farashin Kayan bukatun jama'a na yau da kullun tare da haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar, masamman yankin Dosso, jiha daya tilo a Nijar da ta yi iyaka da Bénin har tsawan kilimita 150 daga yammacin Kasar.
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan hauhawar farashin kayyaki da ake fama da shi a Najeriya, wanda ya jefa al'umma masu karamin karfi cikin halin kunci.
A Najeriyar tun bayan janye tallafin man fetir da kuma matsalolin rashin kudaden waje masamman dalar Amurka sun tsunduma kasar cikin mummunar hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, lamarin da ya jefa al’ummar kasar musamman masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.
Alkaluman hukumar kididdigar Najeriya na watan Satumba sun nuna cewa hauhawan farashin kayayyaki ya kai kashi 26.72, wanda masana ke gargadin zai iya kaiwa da kaso 30 cikin 100 nan da watan Disamba muddun ba’a kai ga gano bakin zarenba.
Domin duba girman matsalar hauhawan farashin, RFI Hausa ya leka kasuwar Mile 12 International dake birnin Legas, daya daga cikin manyan kasuwannin kayan abinci da gwari a kasar.
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda tsadar abincin kaji ke tilastawa masu kiwon su rufe gonaki a tarayyar Najeriya, sakamakon asarar da suke tafkawa.
Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan sake bude kasuwar Monday Market mai matukar muhimmanci a jihar Borno ta tarayyar Najeriya.
Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan jan hankali da kungiyoyi irinsu CISLAC ke yi a Najeriya, wajen ganin gwamnati ta maida hankali kan gibi da ake samu a fannin tara haraji domin samun kudaden shiga.
Masana sun yi ittifakin cewar Najeriya na da dimbin arzikin da bai kamata ace sai ta ciyo bashin kudade kafin biyan bukatun ta ba, amma sakaci da kuma cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu ke mayar da ita baya.
Wannan yasa kungiyar CISLAC mai zaman kanta da ke sa ido kan ayyukan majalisar dokoki da kuma yaki da rashawa, da hadin guiwan cibiyar horar da ‘yan majalisun dokoki da demokuradiyya, suka shirya taro don horarwa da nunawa ‘yan majalisu rawar da za su taka wajen yin dokoki da saka ido a hanyoyin samar da haraji ga kasa.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan bukin cika shekaru 15 cibiyar bada lamuni da raya kasashe ta kasar Faransa Proparco ta yi ta na gudanar da ayyukanta a Najeriya, inda ta zuba jarin da ya kai dala biliyan daya a kasar cikin shekarun. Shirin zai mayar da hankali ne kan yadda ayyukan cibiyar ke bayar da gudunmawa ga fannonin daban-daban na ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Tun bayan kafa cibiyar a shekarar 2008 a Najeriya, Proparco ta mai da hankali wajen hadin gwiwa da cibiyoyin hada-hadar kudi na cikin gida da na wasu kasashen Afirka wajen zuba hannun jari ga kamfanoni masu tasowa da sabbin kafuwa a fannin makamashi mara gurba da muhalli da harkokin noma da kere-kere da kiwon lafiya da dai sauransu…
Shirin 'Kasuw akai Miki Dole na wannan makon ya tattauna ne kan yunkurin gwamnatin Najeriya na rage cunkuso a tashar jiragen ruwan ta Apapa da ke birnin Legas, wajen kaddamar da aikin soma kwashe kwantenoni daga tashar zuwa Ibadan da jirgin kasa na zamani.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners