
Sign up to save your podcasts
Or


Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan makon ya yi duba ne akan hasashen masana game da makomar tattalin arzikin Najeriya a shekarar nan ta 2025.
Masana dai sun daɗe da bayyana wasu hanyoyi da ake amfani da su wajen hasashen makomar tattalin arziƙin ko wacce kasa, yanki ko nahiya a faɗin duniya.
Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....
A wannan mako shirin ya tattauna ne kan rawar da kasuwancin Intanet ke takawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasashe irinsu Najeriya.
Kasuwanci ta internet da ake kira da e-commerce a turance, na taka muhimmiyar rawa wajen sauya yadda ake gudanar da harkokin siye da siyarwa a duniya tare da habakar tattalin arziki.
A Najeriya, masana sun yi ittifakin cewa kasuwanci internet wato e-commerce na kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar, tare da samar da ci gaba ta fuskoki da dama, da kuma samar da ayyukan yi a tsakanin al’ummar kasar.
Duk da cewa an hakkikance kasuwanci ta internet na bunkasa tattalin arziki a Najeriya, akwai tulin kalubale da ya kamata a magance, masamman karancin wayewa game da harkokin kasuwanci ta Internet ga jama'a, da wargajewar kasuwa.
Masana sun yi nuni da cewa, kasuwanci ta internet na bayar da damar da za ta iya haifar da ci gaban tattalin arziki a Najeriya, amma hakan na bukatar tallafi da aiwatar da wasu manufofi, wandanda za su samar da kyakkyawan yanayi ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki ta yadda al'ummar kasar za su dara.
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan asarar da ƴan kasuwar Kantamanto na ƙasar Ghana suka tafka sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar ƙurmus.Hukumomi a Ghana sun ce mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025 ta lakume sama da shaguna dubu 7 tare da tagayyara ƴan kasuwa sama da dubu 30, inda akalla mutun guda ya mutu wasu 14 suka jikkata.
Shirin kasuwa akai miki dole zai mayar da hankali ne kan yadda farashin kayan abinci ya ke hauhawa a Najeriya, daidai lokacin da ake shirye shiryen bukukuwan Kirsimeti, musamman a kudancin ƙasar, inda a halin yanzu farashin buhun albasa yakai sama da ₦320,000 yayin da buhun shinkafa ƴar gida yakai ₦120,000.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........
Wani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku a yawan basususun kasashen ketare, bayan da ta ƙarbi sama da dalar Amurka biliyan 16.5 kwankwacin naira Triliyan 27 da biliyan 700.
Da wannan matsayi Najeriya ta na biye ne da ƙasashen Bangladesh mai matsayi na ɗaya da Pakistan ta biyu a yawan basussuka a duniya.
Sabon ranceHakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar dattawan najeriyar ta sahalewa shugaba Tinubu karbo sabon rancen naira Tiriliyan 1 da biliyan 700, duk da ikirarin ƙasar na samun ƙudin haraji mai yawa daga hukumar kwastom da sauransu.
Yawan basussukaBayaga bankin duniya duniya, jummular basussukan da Najeriya ta ƙarbo ya kai naira triliyan 138, wanda hasashe ma ke cewa zai kai dala biliyan 45 kafin karshen wannan shekara ta 2024.
'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta.
Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin Najeriya, domin ana sayar da nau'ikan dabbobi da suka hadar da shanu, raƙuma, dawaki, tumaki, awaki da jakkai sama da miliyan biyu a ranakun Alhamis din ko wanne mako, kuma yan kasuwa daga sassan Najeriya, Nijar da kuma Mali na zuwa a duk mako.
Shirin kasuwa a kai miki dole na wanna mako ya yi tattaki zuwa taron masu ruwa da tsaki ne a fannin bunkasa tattalin arziki ta kafofin internet wadda a turance ake kira digital economic wanda aka gabatar a jihar Lagos a tarayyar Najeriya.
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali ne kan hada-hadar kasuwaci tsakanin Najeriya da makwabciyarta Kamaru, da irin kalubalen da ƴan kasuwar Kamaru da diribobi daga ƙasashen biyu ke fadi tashi a kan iyakokin ƙasashen biyu. Ƴan kasuwar ƙasashen biyu na amfana da juna, a wasu manyan hanyoyin 10 da a hukumance aka san da su da suka hada na mota da kuma ruwa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tasarin tattalin arziki da ambaliyar baya-bayan nan ya haifarwa jihar da ma al'ummarta.
Makonni biyu kenan tun bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu anguwannin birinin maiduguri na jihar Borno da kewaye, a ranar 10 ga wannan watan Satumba, iftila'in da ya haifar da asarar rayuwa da dukiyoyi mai tarin yawa, tare da lalata gidaje da kasuwanni, inda mutane da yawa suke nemi mafaka a wasu sansanonin yan gudun hijara na wucin gadi, yayin da wasu ke gararamba a kan tituna.
Shirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matsi da tsadar rayuwa da kuma yadda wannan matsala ta jefa kaso mai yawa na magidantan Najeriya a halin tsaka mai wuya, matsalar da ke da nasaba da sabbin manufofin gwamnati ciki har da ƙarin farashin man fetur.
From the publisher's feed
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin…

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners

0 Listeners