Wani matashi dan Najeriya dan asali jihar Borno mai suna Mustafa Abubakar Gajibo ya shiga jerrin mutane da za su daukaka Najeriya ta fuskar kere-keren zamani, wannan matashi ya samu kera motoci masu amfani da hasken rana. Wakilin mu daga jihar Borno, Bilyaminu Yusuf ya samu ganawa da Injiniya Mustafa Abubakar Gajibo da ke Maiduguri wanda ya kera irin wadanan motocin guda 7.