Shirin 'Al'adunmu Na Gado' ya mayar da hankali ne a kan tanade-tanaden al'adun Bahaushe, wadanda akasarinsu suka rungumi addinin Musulunci a game da tamakekeniya a lokacin azumin watan Ramadan. Shirin ya leka kasar Togo, inda ya tattauna da Hausa da ke zaune a wannan kasa tare da wasu kabbilu a game da hakan.