Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya yi duba kan tsananin tsadar tumatir da ake gani a sassan Najeriya musamman yankin kudancin kasar wanda ya dogara da yankin arewaci gabanin samun kayan gwari inda rahotanni ke cewa farashin kwandon tumatur ya ninka fiye da sau 3 na farashin da aka saba sayen shi a baya.