Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya leka garin Mai Tsidau ne a Karamar hukumar Makodan Jihar Kano ta arewacin Najeriya, dan kawo muku yadda wata baiwar Allah mai suna Coach Fatima, wadda ta zamo mace daya tilo da ke horas da kungiyar kwallon kafa ta maza, wadda zancen nan da ake tuni labarinta ya karade kafafen sada zumunta a Najeriya.