A cikin wannan shirin, Azima Bashir Aminu ta yi nazari ne a kan cutar nan ta idanu da ke barazana ga al'umma. An yi kiyassin cewa a duk shekara, ana samun mutane dubu 3 da ke kamuwa da wannan cuta, wanda aka ce idan ba a kula ba tana makantarwa. Shirin ya tattauna da kwararre da kuma wadanda cutar ta addaba.