Shirin 'Duniyar Wasanni' na wanna makon ya yi nazari ne a ka gazawar babbar tawagar kwallon kafar Najeriya wajen samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar nan gaba a wannan shekarar. Najeriya dai ta fafata ne da Ghana a wajen neman wannan tikiti, kuma bayan tawagogin biyu sun buga canjarars a can kasar Ghana, tawagar Ghana ta biyo ta Najeriya har gida, a filin wasa na Moshood Abiola ta karbi wannan tikitin a haduwa ta biyu.