Muhallinka Rayuwarka

Dalilin da ya sanya gwamnonin Najeriya saye amfanin gonar da aka girbe


Listen Later

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe.

A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara  da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Ƙungiyar gwamnonin, kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi bayani tare da ƙarin haske a kan aniyar gwamnonin.

Sai dai kungiyar Manoman ƙasar wato AFAN, ta bakin kakakinta Muhammad Magaji, ta bayyana cewa ba sabon abu bane yadda ake fitar da kayan amfanin gona zuwa ƙasashen waje domin neman riba, amma ta ce ƴan kasuwa da ke sayen kayan a hannun manoman ne ke yin hakan ba manoman da kansu ba.

Kasancewar matakin da gwamnonin su ka ce sun fara ɗauka na sayen kayan abinci su na adanawa na da buƙatar fashin baƙi daga masana, mun tuntuɓi Malam Abubakar Lawal Kafinsoli na sashen nazarin noma a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina dangane yadda hakan zai taimaka wa manoma da kuma harkar noma a ƙasar, wanda ya ce wannan ba hanya ba ce mai bullewa ba, musamman ga talakawan kasar.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.

...more
View all episodesView all episodes
Download on the App Store

Muhallinka RayuwarkaBy RFI Hausa


More shows like Muhallinka Rayuwarka

View all
Labarai by RFI Hausa

Labarai

0 Listeners

Al'adun Gargajiya by RFI Hausa

Al'adun Gargajiya

0 Listeners

Ilimi Hasken Rayuwa by RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

0 Listeners

Dandalin Fasahar Fina-finai by RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

0 Listeners

Kasuwanci by RFI Hausa

Kasuwanci

0 Listeners

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare by RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

0 Listeners

Lafiya Jari ce by RFI Hausa

Lafiya Jari ce

0 Listeners

Tambaya da Amsa by RFI Hausa

Tambaya da Amsa

0 Listeners

Tarihin Afrika by RFI Hausa

Tarihin Afrika

0 Listeners

Wasanni by RFI Hausa

Wasanni

0 Listeners