Shirin na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali ne game da fafutukar kasashen Najeriya da Ghana ta neman gurbi a gasar cin kofin duniya bayan canjaras din da suka yi babu kwallo a wasansu na makon jiya da ya gudana a birnin kumasi, dai dai lokacin da suke shirin haduwa a zagaye na biyu na wasan gobe talata a birnin Abuja na Najeriya.