Shirin Duniyar Wasanni' ma wannnan mako ya mayar da hankali ne kacoka a kan gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya inda yanzu haka ta kai matakin sili daya kwale. A halin da ake ciki, tawagar kasashe da dama dai sun koma gida sakamakon cire su da aka yi. Fitattaau daga cikin su sune, tawagar kwallon kafar Jamus da Brazil. Shirin ya duba yadda gasar ke tafiya da yadda manazarta wasan kwallon kafa ke kallonta.