Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon zayyi nazari ne akan gasar lik din da hukumar kulada kwallon kafar Turai UEFA ta samar, wacce ake kira da ‘UEFA Nations League’ kuma ana bugata ta ne lokacin hutun bazara don ta maye gurbin wasannin sada zumuncin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke shiryawa a irin wannan lokaci, amma kuma wasannin gasar basa shafar wasannin sharan fagen zuwa gasar lashe kofin duniya ko kuma na gasar Turai.