Shirin Ra'ayoyin Masu Sauraro na wannan rana ya bai wa masu sauraro musamman wadanda ke zauna a Libya, damar bayar da karin bayani kan halin da ake ciki dangane da ci gaba da gudanar da ayyukan ceto, yayin da kasashen duniya ke kan isar da kayayyakin agaji ga dubban mutanen da suka tagayyara sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta afka wa wasu yankunan kasar Libya.