Shirin Lafiya jari ce tare da Azima bashir Aminu a wannan mako ya mayar da hankali kan illar cutar cizon mahaukacin kare da aka fi sani da zangai ko kuma Rabies a turance, cutar da mutum kan dauka da zarar karen da ke fama da wata nau'in cuta ya cije shi, ko da ya ke akwai dabbobi da dama da ke haddasa kamuwa da cutar.