Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim ya tattauna ne kan shirin gwamnatin jihar Borno ta Najeriya na ilmantar da marayu a daidai lokacin da Hukumar UNICEF ta ce, sama da yara miliyan 10 ne ke zaune a gida ba tare da zuwa makaranta ba a Najeriya, kuma akasarinsu na rayuwa ne a yankin arewacin kasar.