Shirin 'Kasuwa A Kai Miki Dole' ya yi nazari ne kan tasirin janye tallafin man fetur a kan tataalin arzikin Najeriya, da irin halin da 'yan kasar suka sshiga tun bayan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki wannan mataki. Daya daga cikin bangaarorin da wannan mataki na gwamnatin Najeriya ya shafa shine bangaren harkokin sufuri, ganin yadda farashin shiga abin hawa ya tashi. A wasu sassan kasar wasu masu motoci sun sayar da ababen hawansu inda suka maye gurbinsu da babura ko kekuna.