Shirin na yau ya duba ranar Masoya ta duniya ko kuma Valentines Day a turance wadda ke gudana a duk ranar 14 ga watan Fabarairu, sai dai a wannan karo bikin wannan rana da matasa kan gudanar ta zo a wani yanayi da jama'a ke kokawa da tsadar rayuwa baya ga tashin farashin kayayyaki ciki kuwa har da kyautukan da masoya kan bai wa juna a irin wannan lokaci.