Dai dai lokacin da hukumar INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zabe a Najeriya, wasu jam’iyyu sun fice daga dakin tattara sakamakon zaben saboda zargin hukumar da kin sanya sakamakon a rumbunan adana bayananta, yayinda a bangare guda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke kira da soke zaben wasu yankunan kasar batuun da tuni gwamnatin Tarayya ta gargade shi kan yunkurin tayar da hankula.