Dai dai lokacin da zaben Najeriya ke karatowa, shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi duba kan yadda siyan kuri'u ke kokarin yin tasiri a babban zaben na bana, lura da rashin takardun kudi a hannun jama'a da ma yadda matakin sauya fasalin kudin kasar na Naira ya kara talauci baya ga kassara kananun sana'o'i a sassan kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika.