Kasashen da dama a Afirka ta yamma da na Sahel za su fuskanci ruwan sama masu yawan gaske da ambaliya ,wannan hasashe daga masana na zuwa a dai-dai lokacin da ake kawo karshen taron hukumar kulla da yanayi na kasa a Najeriya Nimet a Abuja.Nasiru sani ya samu tattaunawa da masana dangane da wannan hasashe a cikin shirin Muhalinka rayuwarka daga Rfi.