Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan yadda farashin kayan masarufi ke hauhawa a lokacin azumin watan Ramadana a kowace shekara musamman a manyan biranen Najeriya. A mafiya yawan lokuta farashin kayayyakin masarufi, kayan abinci da na sha, na fuskantar tashin gwauron zabo bisa la’akari da bukatun kayan don yin amfani da su a lokacin azumi.