Shirin Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya tattaunawa kan Cutar Sankarau dake addabar al'umma a Arewacin Najeriya masamman a irin wannan lokaci da yankin ke fuskanctar tsananin zafi ko kuma farkon zubar ruwan sama, yanayin da kan haddasa bullar cutuka daban-daban kama daga Sankarau, kyanda kwalara da kuma zazzabin cizon sauro wadanda a lokuta da dama kan haddasa asarar dimbin rayuka.