Kungiyar PSG ta sanar da cewar Lionel Messi ya sanya hannu a kwangilar shekaru biyu bayan barin kungiyar Barcelona inda ya kwashe shekaru 21 yana mata wasa.PSG za ta dinga biyan sa Euro milyan 40,Abdoulaye Issa a cikin shirin Duniyar wasanni ya duba alfanun zuwa Messi PSG da ma irin kalubalen dake gaban sa.