Gwamnatin Najeriya, ta kawo karshen haramcin bai wa ‘yan kasuwa da ke shigar da kayayyaki iri daban daban har 43 damar samun dalar Amurka daga babban bankin kasar CBN, matakin da ta ce tadauka domin sauwaka wa ‘yan kasuwa da nufin karya farashin kayayyakin da suka hada da na abinci, gine-gine, sabulu, magunguna da dai sauransu a kasar.