Shirin "Muhallinka Rayuwarka" a wannan makon ya yi duba ne kan matsalolin zaizayar kasa, da ke samu a yankin Niger Delta da ke shiyar kudu maso kudancin Najeriya. Jahar Cross River na daya daga cikin jahohin da ke fama matsalar musamman a wani bangare na babban birnin ta Calabar.