A Najeriya ana ci gaba da cece-kuce a kan yadda ake zargin Hukumar Kula da Kudaden Fansho wato PENCOM da biyan kowanne ma’aikacinta albashin akalla Naira miliyan 2 da dubu 400 a kowanne wata a daidai lokacin da tsoffin ma’aikatan da suka yi ritaya bayan hidimtawa kasar ke shan wahala wajen neman a biya su hakkokinsu.