Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mai da hankali ne kan rahotan Hukumar Kididdiga ta Najeriya NBS da ta ta shelanta sake tsundumar kasar cikin wani kangin hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni, lamarin da ya jefa al’ummar kasar musamman masu karamin karfi cikin mawuyacin hali.