Har yanzu shirin 'Duniyar Wasannin' na kasar Qatar, inda ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin duniya. Gasar taa bada mamaki ainun, duba da yadda akasarin kasashen da ake ganin za su kai baanteensu a gasar suka gaza taka rawar gaban hantsi. Yanzu haka gasar ta shiga mako na karshe, bayan da aka samu kasashen da za su fafata a matakin kusa da karshe. A ranar Lahadi ce za a buga wasan karshe na wannan gasa a tsakanin wadanda suka yi nasara a matakin kusa da karshe.