Shirin 'Duniya Wasanni' na wannan makon ya duba yadda aka fafata a wasannin karshe na matakin rukuni a gasar kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Qatar. A nahiyar Afrika, kasashe kamar su Kamaru, Ghana, Senegal da Tunisia sun fice daga gasar a matakin rukuni. A nahiyar Turai, manyan kasashe kamar Jamus da Belgium sun yi waje.