Taron shugabannin kasashe 5 na yankin Sahel da ya gudana ranar lahadi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya jaddada muhimmancin ci gaba da hulda da kasashen duniya don yaki da ta’addancin a yankin na Sahel.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da, a wasu kasashe aka fara nuna shakku dangane da irin rawar da dakarun kasashen yammacin duniya ke takawa a wannan yaki.
Menene ra’ayoyinku game da amfani ko rashin amfani dakarun kasashen ketare a wannan yaki?
Anya yankin Sahel zai iya tabbatar da tsaron kansa ba tare da gudunmuwar kasashen ketare ba?
Kan wannan batu muka baku damar tattaunawa da musayar ra’ayoyi.