Shirin ra'ayoyin Masu Sauraro na wanna rana tare da Khamis Saleh, ya tattauna ne a kan, yadda matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya ke cigaba da daukar wani sabon salo, musamman yadda ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke zirga-zirga a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, lamarin da yayi sanadiyar asarar rai da kuma yin garkuwa da wasu.