Shirin 'Ra'ayoyin Masu Sauraro' na wannan rana ya tattaunawa akan zanga-zangar da maniyata aikin Hajji daga kasar Ghana suka yi, saboda abinda suka kira tsadar kujerar tafiya Hajjin, a daidai lokacin da hukumomin Najeriya da Nijar ke kokarin bayyana dalilan da suka sa aka samu karuwar farashin tafiya Hajjin.