Yanzu haka shugabannin kasashen duniya sama da 50 da shugabannin hukumomin kasa da kasa daban-daban, da kungiyoyi masu zaman kansu, sun hallara a birnin Paris na Faransa, domin tattauna yau Alhamis da ake fara taron duniya don shimfida tsarin da zai bai wa kasashen damar samun tallafi da nufin tunkarar matsalar sauyin yanayi.