Bayan kwashe shekaru 18 ana tafka shari'a a kan rikicin Masarautar Gindiri dake Jihar Filato a Najeriya dangane da nadin Sum Fyem, kotun kolin Najeriya a karshen ta yanke hukunci wanda ya sabawa umurnin da ta bayar a baya. A cikin wannan shrin Abdoulayye Issa yayi bitar rikicin da kuma matsayin da kotun ta dauka akai.