Shirin ra'ayoyin masu saurare tare da Hauwa Muhammad a kowacce juma'a ya na baku damar tofa albarkacin bakinku kan duk wani batu da ke ci muku tuwo a kwarya, kama daga tattalin arziki, tsaro da ci gaban yankunan da kuka fito, ko kalubalantar salon kamun ludayin gwamnatoci ko kuma jinjina. Ayi saurare Lafiya.