Bincike dai ya nuna cewa gajen hakuri tsakanin al'umma, ya haddasa barkewar rigingimu tare da tafka asara bila adadin a wurare da dama, wannan ya sa hukumar raya Ilmi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta bude asusun samar da kudade na musamman domin wanzar da tasirin hakuri da juna a kasashen da ke fama da tarzoma, ciki har da kasashen Afirka.